July 28, 2021

AMMAR BIN YASIR

AMMAR BIN YASIR

 

Gabatarwar Mujtaba Adam:

“Baya ga kasantuwar Ammar Bin Yasir sahabin Ma’aikin Allah wanda ya bada imani da shi, tun a shekarun farko na bayyanar Musulunci, yana kuma daya daga cikin wadanda su ka taka gagaruwar rawa ta fuskar tsarin zamantakewar al’ummar musulmi.

Wannan, ya maida shi zama daya daga cikin wadanda manazarta masu mahanga daban-daban su ka maida hankali wajen yin bincike akan rayuwarsa. Wannan bayanin da zai zo a kasa, daya ne daga cikin nazarin da aka gudanar akan Ammar. Wanda ya yi shi, mai suna Farfesa Aliyul-Wardi, malamin ilimin zamantakewa ne (Sociology) na kasar Iraki. Ya kuwa maida hankali ne wajen yi wa rayuwar Ammar fida ta fuskar ilimin zamantakewa ba ta fuskar akida ba.

Kuma saboda kasantuwar nazarin yana da tsawo, sannan kuma da la’akari da gandar karatu da mafi yawancin Hausawa su ke da shi, an karkatsa shi da kuma bai wa bangarorinsa jigo-jigo domin jan hankalinsu su daure su karanta.

Sai dai shakka babu da akwai izina mai yawa ga rayuwar wannan bawan Allah, ga wanda ya ke son daukar izina, sannan kuma da sharhi ba irin wanda aka saba da shi ba akan yadda al’ummar musulmi ta kasance a daidai lokacin da Ammar din ya ke rayuwa.

Da fatan za a ji dadin karatu da kuma daukar izina.

 

                       Nuna wa Ammar Wariyar Launin Fata:

 

Idan mu ka yi nazarin rikicin da ya barke a tsakanin Kuraishawa da talakawa  a lokacin Usman, to za mu ga cewa Ammar Bin Yassir ya taka rawa mafi muhimmanci aciki. Watakila rawar da Ammar ya taka a lokacin wannan rikicin ta dara ta kowane mutum ta wata fuska. Ya dace mu fadi cewa ya fi Abu Zar tsanani a cikin gwagwarmayarsa da Usman haka nan kuma ya fi shi yin magana gaba-gadi da kuma yin fito na fito. Ya kuwa fuskanci wahala mai tsanani sanadiyyar hakan.

Zubin zatin Amma ya banbanta da na Abu Zar ta fuskoki da dama. Abu Zar balaraben  kauye ne da ya fito daga kabilar da ta ke rayuwa a tsakiyar sahara- ita ce kabilar Gaffar. Shi kuwa Ammar ‘yantaccen bawan birni ne wanda aka haife shi a makka ya kuma yi rayuwa mai tsawo a matsayin bawa.

Launin fatar Ammar wankan tarwada ne ko kuma wanda ya yi kama da baki. Ya gaji wannan launin fatar tashi ce daga mahaifiyarsa wacce ‘yar Habasha ce. Wani abu da ya dace a yi ishara da shi anan shi ne cewa a wancan lokacin larabawa suna wulakanta wanda launinsa ya ke wankan tarwada ko baki.  Farin launi yana daga cikin alamar daukaka a wurinsu. Idan su ka yabi mutum sai su ce masa: “Mai farin hannu” Idan kuma suna son su yi ishara da wasu mutane da su ke yabawa sai su fadi cewa: “Mu nufi wurin fararen mutane.”

Watakila kin jinin bauta da larabawa su ke yi ne ya sa sami wannan tunanin.  Bakin launi shi ne launin mafi yawancin bayi. Har a wannan lokacin kabilun larabawan kauye a Iraki suna kaskantar da wanda ya fito daga tsatson bayi. Wanda duk ya zagi wani ta hanyar dangata masa bauta to ya cancanci a yi masa ukuba. Ammar Bin Yassir ya rayu cikin wannan matsalar.

Kuraishawa sun rika aibata Ammar da cewa shi: “ Bakin bawa” ne. A lokacin da  Marwan ya zuga Usman da ya kashe shi  ya aibata shi da cewa: “ Wannan bakin bawan ne ya tunzura mutane akanka. Idan ka kashe shi to ka yi maganinsa. Sai su ka yi masa duka har sai da ya suma.” ( Abqariyyatul-Imam: Abbas Aqqad.)

Khalid Bin Walid ya kai karar Ammar a wurin annabi sai ya fada masa: “Wannan bakin bawan.” ( Ammar Bin Yassir: Abdullah al-Subaiti.)

A lokacin yakin Siffain Mu’awiyya ya yi magana akansa yana cewa: “ Larabawa sun halaka idan su ka biyewa bakin bawa.”  ( Littafin da ya gabata.)

Ammar da ya ke kare kansa a gaban Kuraishawa a wannan rana ya fadi cewa: “ Mutum mai girma shi ne wanda Allah ya girmama shi. Na kasance kaskantacce sai Allah ya daukaka ni. Na kasance bawa sai Allah ya ‘yantar da ni. Na kasance mai rauni sai Allah  ya karfafani. Na kasance talaka sai Allah ya wadata ni.” Ammar ya yi wannan magana ne a lokacin da Amru Bin As ya aibata shi da bakin launin fatar mahaifiyarsa. ( Littafin da ya gabata.)

Dalilan da Ammar ya kafa dalilai ne irin na mutane karabiti wadanda suka taka matakalan kaiwa ga daukaka da kansu. “Ya’yan mutane masu jan wuya da matsayi ba su fahimtar wannan irin dalilin. Masu jan wuya suna daukar matsayin da su ke da shi abin fankama kuma suna jin cewa shi ne komai. Ba su daukar cewa gina kai da mutum zai yi ya fi dangatakarsa ta jini da matsayi, kima ba.

Ammar yana hake da Kuraishawan da su ka azabtar da shi kuma su ke yi masa girman kai da kuma aibata shi da mahaifiyarsa. Yana daukar mahaifiyarsa da ta ke shahidiyar farko a Musulunci a matsayin tushen alfahari a gare shi. Su kuwa kuraishawa suna daukr ta a matsayin tushen kaskanci a gare shi. Yana kiran kansa “Dan shahidiya” su kuma suna kiransa “Dan Bakar mace”

Matsalar biladama ita ce kowanensu yana yi wa lamurra matsayi ne bisa ma’auni nashi na kanshi. Kowane daga cikinsu yana kallon abubuwan bisa yadda ya ke ganin da ya dace da  shi, ya kuma ki jinin wani abu bisa sonsa.

An yi cacar baki tsakanin Ammar da Abdullahi Ibn Abi Sarh a lokacin yi wa Usman Mubaya’a. Ibn Abi Sarh yana goyon bayan Usman sai Abu Zar ya fada masa cewa: “Yaushe ka zama mai yi wa musulmi nasiha?” Sai wani mai  goyon bayan Banu Umayya ya maida masa martani da cewa: “ Ka wuce iyakarka ya kai Dan Sumayya. Ina ruwanka da yadda Kuraishawa za su zabi sarkinsu? “

Suna aibata Ammar da mahaifiyarsa. Zagi mafi muni a wurin balarabe shi ne a danganta mutum da mahaifiyarsa. Suna kiransa “Dan Sumayya.” Suna cewa ya wuce iyakarsa da ya tsoma baki akan yadda iyayengidansa Kuraishawa za su zabi sarkinsu. Shi kuwa yana daukar kansa a matsayin wanda ya ke da fifiko akansu domin kuwa ya sami daukaka da matsayi ne daga Musulunci, saboda haka shi ne wanda ya fi dacewa ya tsoma baki akan yadda za a zabi halifan musulmi.

Ba ya fahimtarsu, su ma ba su fahimtarsa. Kowane bangare yana kallon lamarin ne da mahangarsa ta kashin kansa. Kowane yana da ma’auni na shi na kanshi… Kusurwowi biyu ne da ba za su taba haduwa ba.

 

 

 

 

 

 

 

Daga:

Mallam Mujtaba  Adam

 

Zamu cigaba…

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “AMMAR BIN YASIR”