March 26, 2023

Amfanin citta ga dan Adam.

Citta na daga cikin abubuwan da ake iya amfani da shi wajen girkin abinci da kuma abin sha, kuma yanada sinadari mai kyau. Yanada kyau ayi amfani da shi wajen ko wani abinci domin taimakon lafiyar jiki da kuma kare cututtula iri-iri.

Ga amfanonin citta :

 1. Citta na taimakawa wajen kare sanyi da wasu cututtuka.
 2. Yana taimakawa wajen ɗauke zafin cuta ko ciwon a jiki.
 3. Citta na taimakawa wajen gudanar da yawan siga a jikin mutum.
 4. Citta na taimakawa wajen kawar da zafin ƙirji da zuciya.
 5. Citta na taimakawa wajen rage ƙiba da kuma kwantar da abinci.
 6. Bincike ya nuna cewa citta na taimakwa wajen kare cutan ‘Alzheimer’.
 7. Citta na haɓaka gudanar jini a jiki kuma tana ƙara ƙarfi.
 8. Tana taimakwa wajen rage azabar cutan Asthma.
 9. Yana taimakwa wajen warkar da cutan daji.
 10. Tana taimakawa wurin sarrafa abinci: Citta na taimakawa wurin sarrafa abincin da muke ci kuma tana taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa garkuwan jiki.
 11. Citta na tsarkake bakin mutum ta hanyar samar da yawu wanda ke taimakawa wurin sarrafa abinci.
  12 – Magance zafin ala’dar mata (Dysmenorrhea). Galibin mata sukan yi fama da ciwon ciki yayin da al’adarsu na wata ya zo kuma ɗaya daga cikin abubuwan da ake amfani da shi wurin sauƙaƙe zafin ciwon shine citta. Ana iya shan ruwan citta kafin al’ada ko cikin kwanakin Al’adar.

13.Yaƙi da cutar daji da rage tsufa: Citta na ɗauke da wasu sinadarai masu yaki da cututuka a jiki wanda ake kira ‘Antioxidants’ wanda suke taimakawa wurin magance kansa musamman ta mahaifa. Kazalika, antioxidant na taimakawa wurin kare fatar jikin dan adam daga lakumewa.

14 – Magance tashin zuciya: Akwai tarihi da binciken masanana masu yawa game da amfani da citta wurin magance tashin zuciya da rashin sha’awan cin abinci. Hakan na faruwa ne saboda citta yana hana tashin zuciya da amai.

15 – Daidaita adadin siga a jinin dan Adam: Binciken masana ya nuna cewa citta yana taimakawa wurin daidaita yawan siga a jinin mutum. Wannan yana da muhimmanci saboda yawan siga da ke jinin dan adama yana da alaka da kara ƙiba ko rage ƙiba.

Domin samun cikakkaen amfaninsa, ayi amfani da danyen citta.

©blue print.

 

SHARE:
Kiwon lafiya 0 Replies to “Amfanin citta ga dan Adam.”