July 31, 2021

AMBALIYAR RUWA A KANO TA LALATA FIYE DA GIDAJE 1,000

Daga Baba Abdulkadir

 

Hukumar nan da ke bada agajin gaggawa ta jihar Kano wato SEMA, ta ce, kimanin mutane 26 ne suka mutu, kana gidaje fiye da dubu ɗaya suka lalace sakamakon ambaliyar ruwa a kananan hukumomin jihar 4 na Kano,

 

Shugaban hukumar Alhaji Saleh Jili ne ya  bayyana hakan ga manema labarai a Kano, inda ya ce, an tattara alƙaluman iftila’in ne daga watan Afrilun da ya gabata zuwa wannan wata na Yuli da muke bankwana da shi.

 

Kazalika ya ƙara da cewa, zuwa yanzu akwai kimanin mutane hamsin da suka jikkata sakamakon ambaliyar.

 

Sale Jili, ya ce ƙananan hukumomin Bunkure da Minjibir da Tarauni da kuma ƙaramar hukumar Doguwa ne ke kan gaba wajen iftila’in na bana anan jihar Kano.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “AMBALIYAR RUWA A KANO TA LALATA FIYE DA GIDAJE 1,000”