January 22, 2023

Alummar Kasar Borkina faso Sun Bukaci Sojojin Faransa Su Fice Daga Kasarsu

 

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin soji ta kasar Borkina Faso ta shaidawa kasar Faransa da ta janye dukkan sojojinta daga kasarta cikin wata daya, bayan da aka gudanar da gagarumar zanga-zangar neman ficewar sojojin a kasar.

Gwamnatin borkina faso ta yi tir da yarjejeniyar da aka kulla tun a shekara ta 2018 tsakanin faransa da tsohuwar gwamnatin kasar na kasancewar sojojin faransa a kasar , don haka ta basu wa’adin wata guda da ta kwashe dukkan dakarunta a kasar

Kasar faransa ta aike da dakaru fiye 400 zuwa kasar Borkina faso karkashin yaki da ta’addancin, da ya haddasa mutuwar mutane da dama tare da tilastawa sama da miliyan biyu barin gidajensu ba shiri.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Alummar Kasar Borkina faso Sun Bukaci Sojojin Faransa Su Fice Daga Kasarsu”