March 26, 2024

Al’umma sun Fusata biyo bayan bidiyon kudaden fansa da Yan bindiga suka wallafa a shafukan sada zumunta

 

An wayi gari da cece-kuce da tofin Allah tsine da jama’a ke yi kan faifan bidiyo da ke nuna wani dan bindiga ke bayyana kudaden fansa da ya karbo daga hannun yan uwan mutanen da ya yi garkuwa da su.

Ya wallafa wannan faifan bidiyon ne a manhajar Tiktok. Inda a bangare guda wani kwararre a bangaren fashin baki mai suna Zagazola Makama ya wallafa bidiyon a shafinsa na Tuwita inda kuma yace wanda ya wallafa wannan bidiyo na farko da ake zargin Dan bindiga ne na da mabiya sama da 3000 a shafin sa na Tiktok, inda yace mafi yawansu yan bindiga ne da suke nuna makaman su a fili.

Zagazola ya kara da cewa Manhajar TikTok ta zama wata fage ta da ke yada fasadi da lefuka ba tare da wata shamaki ba.

Lamarin tsaro dai na ta kara tsamari a Najeriya musamman a yankunan Arewacin kasar, sai dai kuma kokarin gwamnati na dakile wannan munanan lefuka ya ‘karanta kamar yadda masu sharhi ke bayani biyo bayan bayyanar wannan faifan bidiyo.

 

 

 

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Al’umma sun Fusata biyo bayan bidiyon kudaden fansa da Yan bindiga suka wallafa a shafukan sada zumunta”