January 19, 2023

Alkalan kotun Shari’ar Musulunci a Kano sun lamushe kudin marayu

Alkalan kotun shari’ar Musulunci da ma’ajiya da  akawu har ma da wasu ma’aikanta 14, sun gurfana a gaban kotun Majistre da ke birnin Kano na Najeriya bisa zargin su da wawure kudin marayu da ya kai kusan Naira miliyan 500.

A zaman kotun na Majistre wanda babban alkalinta, Mustapha Sa’ad ya jagoranta, an bayyana cewa, ana zargin wadannan mutanen da aikata babban laifi wanda ya kunshi cin-amana, hada-baki da zamba da satar kudi da kuma kwaikwayan sa-hannu.

Wannan laifin mai ‘ya’ya, ya saba wa sashi na 97 da 79 da 315 da 289 na dokar Penal Code.

Bayanan farko-farko sun nuna cewa, a shekarar 2020 zuwa 2021 ne, Bashir Ali  Kurawa da Sa’adatu Umar da Tijjani  Abdullahi da Maryam Jibrin Garba da Shamsu Sani da Hussaina Imam, suka aikata laifin, inda ita Hussaina Imam, ta yi amfani da kujerarta ta ma’ajiyar kotun daukaka kara ta sharia’ar wajen hada-baki da sauran aminanta da aka ambata.

An ce dai ita Hussaina ta saci takarda mai dauke da tambarin kotun tare da kwaikwayan sa-hannun jami’an da ke da izinin cire kudi daga asusun bankin kotun na IBTC domin wawure kudin da ya zarta Naira miliyan 480.

Ma’ajiyar ce kuma ta bada umarnin rarraba kudin cikin wasu asusai na daban ba tare da sani ko  izinin ainihin wadanda ke da alhakin cire kudin ba a hukumance.

An dage zaman sauraren shari’ar har sai zuwa ranar 1 ga watan Fabairu mai zuwa, yayin da aka tasa keyar su zuwa gidan-kaso.

 

©FRI.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Alkalan kotun Shari’ar Musulunci a Kano sun lamushe kudin marayu”