March 25, 2024

Algeria ta aike da tan 150 na agaji zuwa Gaza

 

Aljeriya ta aikewa da tan 150 na agajin jin kai ga Falasdinawa a Gaza, a daidai lokacin da ake gargadin barkewar yunwa a can.

Kayayyakin sun hada da kayan abinci da kayan jarirai.

Ma’aikatar tsaron kasar ta ce “Wannan taimakon yana nuna kudurin Aljeriya na samun hadin kai mara sharadi da mara iyaka ga al’ummar Palasdinu.”

Jiragen saman soja za su yi jigilar kayan agajin a ranar Litinin daga filin jirgin saman soja na Boufarik da ke kusa da Algiers babban birnin kasar zuwa filin jirgin El-Arish na Masar, wanda ke kusa da zirin Gaza.

 

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Algeria ta aike da tan 150 na agaji zuwa Gaza”