November 17, 2022

Akalla mutane 5 aka hallaka a harin yankin Khuzestan ta kasar Iran

Rahotanni dake zuwa na nuna cewa akalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu a harin yankin Kudu ta yammacin kasar Iran.

Kafafen yada labarai sun bayyana hakan a matsayin harin ta’addanci.

 

Tashar talabijin ta kasar Iran ta bayyana cewa wasu mutane akalla 15 sun jikkata bisa harin na kasuwar birnin Izeh.

Rahotannin sun ce wasu yan bindiga biyu ne suka bude wuta kan mai uwa da wabi a tsakiyar kasuwar.

Mutanen da suka rasa rayukan su sun hada da wani yaro da mace guda kana kuma da wasu mazaje uku.

Kamfanin dillanci ta ISNA ta bayyana cewa biyu daga wadanda suka rasu jami’an sa kai ne na Basij.

SHARE:
Labaran Duniya, Rahotanni 0 Replies to “Akalla mutane 5 aka hallaka a harin yankin Khuzestan ta kasar Iran”