January 7, 2023

Adamawa: An tsaurara tsaro gabanin ziyarar Shugaba Buhari zuwa jihar

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta jibge jami’anta da dama don tabbatar da tsaro da kuma kwanciyar hankali a ziyarar shugaba Buhari ga jihar.

 

Hukumar kana ta bada umarnin nuna aikin kwarewa da kuma kariyar hakkin dan adam ga jami’an ta.

 

Mai magana da yawun hukumar a jihar, Sufurtanda Suleiman Ngurejo ya bayyana hakan a yau Asabar a wani bayani da yayi a garin Yola, babban birnin jihar Adamawa.

 

Kamfanin dillancin labarai ta kasa (NAN) ta fitar da rahoton cewa Buhari zai ziyarci jihar ta Adamawa a ranar Litinin mai gabatowa don daga tutar kamfe na ‘yar takarar gwamnan jiha a karkashin inuwar jam’iyar APC Sanata Aishatu Binani.

SP Ngurejo ya kara da cewa, hukumar su ta yan sanda na shirye don yin aikin hadaka da sauran bangarorin tsaro don tabbatar da tsaro a jihar. Ta kuma ce za’a takaita zirga-zirgar ababen hawa musamman masu zuwa daga hanyar Sangere-Numan zuwa garin Yola.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Adamawa: An tsaurara tsaro gabanin ziyarar Shugaba Buhari zuwa jihar”