October 9, 2023

Adadin wadanda suka mutu ya haura 1,100 a yakin Isra’ila da Hamas

 

A kokarin dakarun Isra’ila na sake dawo da doka da oda a wasu yankunan da take kayautata zaton mayakan Hamas suna boye,an gwabza fada tsakanin bangarorin biyu a kewayen zirin Gaza.

Baya ga umurtar mutane su fice daga yankin tareda kwashe wasu daga cikin su ,Firaministan Isra’ala Benjamin Nethanyahu da ke ci gaba da samun sakonnin goyan baya daga manyan kasashen Duniya ya kira dakarun kasar sa da su shirya ga abinda ya kira yaki na dogon lokaci mai wahala.

Adadin wadanda suka mutu a wasu alkaluma da ake da su ya haura 1,100 a rana ta uku na wannan yaki .

KungiyarIsra Hamas ta Falasdinu ta kaddamar da wani harin ba-zata daga Gaza, inda ta harba rokoki tare da aikewa da wasu mayaka wadanda ke rike yanzu haka da kusan fursunoni yan Isra’ila 100.

Hukumomin yankin Gaza sun ba da rahoton mutuwar akalla mutane 413 a cikin fararen hula da kuma killace mutane miliyan 2.3.

Dubun dubatar sojojin Isra’ila ne aka jibge domin fafatawa da mayakan Hamas a kudancin kasar, in da aka gano gawarwakin fararen hula da aka jibge a kan tituna da kuma tsakiyar gari.

Shugaban Amurka Joe Biden ya ba da umarnin “karin goyon bayan ga Isra’ila biyo bayan wannan harin da ya bayyana shi a matsayin ta’addancin da Hamas ta kaiwa Isra’ila.”

Sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin ya ce Washington “za ta yi gaggawar baiwa sojojin Isra’ila karin kayan aiki, gami da alburusai”. Lloyd Austin ya jagoranci jirgin ruwan yaki USS Gerald R. Ford zuwa gabashin tekun Mediterrenean, kuma ya ce Washington na kara yawan dakarun zuwa yankin.

Sai dai kungiyar Hamas ta ce taimakon da Amurka ta bayar tamkar cin zarafin Falasdinawa.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Adadin wadanda suka mutu ya haura 1,100 a yakin Isra’ila da Hamas”