April 17, 2023
Adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar rikicin Sudan ya kai 97

Kungiyar likitoci ta kasar Sudan, ta ce rikici a birnin Khartoum na kasar ya shiga kwana na 3, inda adadin wadanda suka mutu ya kai 97.
Sanarwar da kungiyar ta fitar yau ta ce, daruruwan fararen hula kuma sun jikkata sanadiyyar rikicin.
Rikicin Sudan ya haifar da damuwa tsakanin kasa da kasa, da MDD da kungiyar tarayyar Afrika da kungiyar kasashen Larabawa da sauran hukumomin kasa da kasa, inda suke kira da a tsagaita bude wuta nan take.