December 7, 2022

Abin da ‘yan Najeriya ke cewa kan matakin CBN na taƙaita yawan kuɗin da za a iya cirewa kullum

Yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu game da sabon matakin da babban bankin ƙasar CBN ya ɗauka na taƙaita yawan kuɗin da za a iya cirewa daga asusun ajiyarsu na banki.

A ranar Talata ne dai babban bankin Najeriya CBN ya fitar da sababbin dokoki na hada-hadar kuɗaɗe a bankunan ƙasar.

A cikin sabbin dokokin, CBN ya ce daga ranar tara ga watan gobe yawan kuɗin da mutum ɗaya zai iya fitarwa a banki a sati shi ne naira 100,000 yayin da kamfani zai cire naira 500,000 ne kawai a sati.

Haka kuma CBN ɗin ya ce yawan kuɗin da mutum zai iya cirewa ta hanyar amfani da na’urar cirar kuɗi ta ATM a sati shi ne naira 100,000, wato yawan abin da za a cire a rana naira 20,000 ne kacal a na’uran ATM da kuma wajen masu amfani da POS.

Tun bayan fitar da sabbin dokokin ‘yan ƙasar ke tofa albarkacin bakinsu, a yayin da wasu ke sukar matakin wasu kuma cewa suka yi suna maraba da matakin.

Haka kuma tun bayan da muka wallafa labarin a shafinmu na Facebook ranar Talata da yamma, zuwa ranar Laraba da safe mutum 26,000 ne suka so labarin, sannan kusan mutum dubu bakwai ne suka yi tsokaci game da labarin inda aka raba shi fiye da sau 1,000.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Abin da ‘yan Najeriya ke cewa kan matakin CBN na taƙaita yawan kuɗin da za a iya cirewa kullum”