May 1, 2024

Abel Tesfaye ya ba da ƙarin dala miliyan 2 don tallafawa ayyukan agajin abinci a Gaza,

The Weeknd, a karkashin asusunsa na agaji na XO, ya ba da ƙarin dala miliyan 2 don tallafawa ayyukan agajin abinci a #Gaza, da nufin rage yunwa a tsakanin iyalai masu bukata. Wannan gudummawar, kamar yadda Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ta ruwaito, ana sa ran za ta samar da burodi sama da miliyan 18, wanda zai dauki sama da Falasdinawa 157,000 na wata guda.

Mawaƙin, wanda aka fi sani da sunansa na gaske Abel Tesfaye, a baya ya ba da gudummawar dalar Amurka miliyan 2.5 ga Gaza a cikin Disamba 2023, wanda ya ba da kwatankwacin abincin gaggawa na miliyan huɗu ga fararen hula da abin ya shafa.

Iyalai a Gaza na fama da yunwa sakamakon kazamin kawanya da haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi, tare da hana shigar da bukatun jama’ar Gaza da ke kara tsananta yanayin jin kai a yankin.

#Falasdinu

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Abel Tesfaye ya ba da ƙarin dala miliyan 2 don tallafawa ayyukan agajin abinci a Gaza,”