April 12, 2023

​Abdullahian: Ya Zama wajibi A Gaggauta Daukar Mataki Kan Halin Da Falasdinu Ke Ciki

 

Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir Abdollahian ya aike da sakonni daban-daban ga babban sakataren MDD Antonio Guterres, da babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi, Hossein Ibrahim Taha, da kuma takwarorinsa na kasashen waje na kasashen musulmi, yana mai bayyana matukar damuwarsa dangane da halin da Palastinu ke ciki a halin yanzu sakamakon ayyukan laifukan yaki da yahudawan sahyoniya suke yi.

A cikin wadannan sakonni, ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi bayyana laifukan da yahudawan sahyoniyawan suke aikatawa kan al’ummar Palastinu da suka hada da kisa da kamu da barnata dukiyoyi a matsayin wanda ya sabawa ka’idoji da dokokin kasa da kasa da hakkokin bil’adama.

Sannan ya jaddada cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kakkausar suka ga irin ta’asar da gwamnatin yahudawan Sahyuniya ta Isra’ila take yi kan al’ummar Palastinu, da kuma tauye wa al’ummar Palastinu hakkokinsu da suka hada da ‘yanci da akkinsu na rayuwa.

Ya ce wadannan matakan sun zama misali karara na cin zarafi da keta hakkin bil’adama da kuma nuna wariya

A wani bangare na wadannan sakonni, ministan harkokin wajen na Iran ya yi nuni da cewa, yahudawan sahyoniya sun yi amfani da yadda hankulan al’ummar duniya suka shagaltu da yakin Ukraine, yana mai sukar shuru da rashin daukar mataki na hukumomin kare hakkin bil’adama da kuma kasashen da suke da’awar kare hakkin bil’adama.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Abdullahian: Ya Zama wajibi A Gaggauta Daukar Mataki Kan Halin Da Falasdinu Ke Ciki”