October 1, 2023

Abdullahian Ya Taya Takwarorinsa Na Kasashen Musulmi Murnar Maulidin Manzon Allah (SAW)

 

Ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir Abdollahian, ya aike da sakon taya murnar Maulidin Manzon Allah (SAW) zuwa ga takwarorinsa na kasashen musulmi.

Amir Abdullahian ya bayyana a shafinsa na “X” cewa, yunkurin Imam Al-Khomeini na ayyana makon hadin kan Musulunci ya samo asali ne daga tsarin hadin kan musulmi da kuma haduwar gwamnatocin Musulunci don cimma matsayi mafi girma na dan Adam.

Ya kara da cewa, ina mika sakon gaisuwata ga al’ummar musulmin duniya da malamai na kasashen musulmi dangane da haihuwar manzon rahama da rahama Muhammad (SAW).

Sannan kuma ya yi fatan samun nasara da albarka da ci gaba da samun bunkasar tattalin arziki ga dukkanin kasashen musulmi baki daya.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Abdullahian Ya Taya Takwarorinsa Na Kasashen Musulmi Murnar Maulidin Manzon Allah (SAW)”