January 16, 2023

Abdollahian : Falasdinu Da Kudus Su Ne Mafi Muhimmanci A Duniyar Musulmi

‘’ A tsawon shekaru, Amurka da kawayenta, sun shirya makirce makirce kala-kala kan wadannan wuraren ta hanyar kula yarjejeniyoyi daban daban, ta baya bayan nan it ace yarjejeniyar Abraham, saidai bisa jajircewa kunmgiyoyin gwagarmaya, Falasdinawa sun cuturar da duk wadannan makirce makircen’’injiAmir-Abdollahian.

Hatta a yayin kofin kwallon kafa na duniya, an nuna goyan baya ga Falasdinu, yayin da kyautata alakar kasashen larabawa da Isra’ila ba da wani mahimmanci ko na dinari guda daya inji shi.

‘’ canza suna ko fasali ba shi da wani tasiri ga Falasdinu, face haifar da rikice rikice ga Isra’ila’’ inji Amir Abdolahian.

Ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke ganawa da bangarori daban daban na al’ummar Falasdinu yayin ziyarasa a kasar Siriya.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Abdollahian : Falasdinu Da Kudus Su Ne Mafi Muhimmanci A Duniyar Musulmi”