March 29, 2023

Abba Kabir Yusuf zai karɓi shaidar zaɓen sa a matsayin gwamnan Kano a yau

Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf na Dar da karɓar shaidar zaɓen sa a matsayin gwamnan jihar a zaɓen gwamna da ya gudana a ranar 18 ga watan Maris.

Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya kada babban abokin karawar sa na jam’iyyar APC, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a yau Laraba ne INEC ta sanya a matsayin ranar da za ta baiwa wadanda su ka lashe zaben gwamna da na majalisun jiha, a kowacce jiha.

Sabo da haka, a yau ne Abba Kabir, na jam’iyyar NNPP, ke karɓar ta sa shaidar, tare da zaɓaɓɓun ƴan majalisar jihar.

Wakilin mu da ke wajen bada shaidar, wanda ke wakana a ofishin INEC na Kano, ya gano cewa an saka jami’an tsaro domin tabbatar da an yi bikin cikin lumana.

Haka zalika an rufe titinan da su ke da kusanci da ofishin na INEC, yayin da magoya bayan jam’iyyar NNPP su ka yi dafifi a kofar shiga ofishin na hukumar zaɓe.

Karin bayani na nan tafe…

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Abba Kabir Yusuf zai karɓi shaidar zaɓen sa a matsayin gwamnan Kano a yau”