January 27, 2024

A Tarihin Musulunci Babu Wanda Ya Sadaka Yana Ruku’u Sai Ali Bin Abi Talib (A.S.).

Ayatullahi Makarim Shirazi ya bayyana hakane  a wajen bikin nada rawani wasu daga ciki daliban makarantar hauza da aka gudanar bayan sallar azuhur a makarantar Amirul Muminin (a.s) inda ya ce: Batun waliyya ya zo a cikin alqur’ani mai girma. Kuma wilayar Amirul Muminina (AS) tana da makiya.

Ya kula da irin girman matsayi na Amirul Muminin (AS) ya ce: A tarihin Musulunci babu wani mutum wanda ya yi sadaka yana ruku’u sai Ali Ibn Abi Talib (AS).

Marja’in ya ci gaba da cewa: Allah ya gaya wa Manzon Allah (SAW) cewa idan har sakon waliyyar Imam Ali (AS) bai isa ga mutane ba, to sakon Manzon Allah (SAW) bai cika ba.

Marja Taqlid ‘yan Shi’a ya ci gaba da cewa: Allah ya jaddada kan batun wilayar Imam Ali (AS) da lafuzza mabanbanta domin wasu ba sa son fahimtar hakikanin fadin Allah.

Ayatullah Makarm Shirazi ya taya matasan daliban murnar zagayowar ranar sanya tufafin malunta inda ya ce: Daga yau aikinku ya yi nauyi kuma hakan ya nuna cewa tufafin malamai na da tasirori masu yawa.

Da yake bayani kan cewa dalibai su gode wa Allah da suka sanya rigar sojan Imam Zaman (A.S) ya ce: Watakila mutane da yawa za su so sanya wannan rigar, amma ba za su iya samun nasarar sanya ta ba, amma ku kuma Allah ya ba ku wannan nasara.

Malamin manyan jami’o’in makarantun hauzar ya bayyana cewa: Ya kamata matasa dalibai su yi kokarin zama sabon mutum daga yau, kuma dabi’ar mu’amalarku da sauran mutane ta canza daga yau, kuma mutane su fahimci kun shiga wani sabon mataki daga yau.

Marjin Taqlidin ‘yan Shi’a ya kara da cewa: Ina rokon ku da ku sami damar sauke hakkin wannan tufafin kuma hakan ba zai yiwu ba sai da yardar Allah ku mika kanku ga Allah.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “A Tarihin Musulunci Babu Wanda Ya Sadaka Yana Ruku’u Sai Ali Bin Abi Talib (A.S.).”