November 8, 2022
A naɗa ministar tsaro mace a ga aiki da cikawa, inji ƴar majalisar wakilai

Taiwo Oluga, shugabar kwamitin majalisar kan mata a majalisa, ta ce ya kamata a naɗa mace a matsayin ministar tsaro domin magance kalubalen tsaro yadda ya kamata.
A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN, Oluga ta yi wannan magana ne a jiya Litinin a wani taron manema labarai da kungiyar Tarayyar Turai tare da hadin gwiwar asusun kula da mata na Nijeriya suka shirya, a Abuja.
Ta ce shigar mata a harkokin siyasa ya yi matuƙar ƙaranci a Nijeriya duk da shawarwarin da kungiyoyi daban-daban ke bayar wa a kasar.
Oluga ta nuna damuwarta kan karancin mata da da a ka zaɓukan fidda-gwani na shugaban kasa da su a bana, inda ta kara da cewa hakan zai hana mata samun nasarar kashi 35 cikin 100 da a ka tabbatar wajen samun mukamai.
“A karon farko a tarihi, a nada mace a matsayin ministar tsaro, za a ga aiki da cikawa; za ku ga canji mai kyau a harkar tsaron mu,” inji ta.
©Daily Nigeria Hausa