January 29, 2023

A Karshe CBN Ya Tsawaita Wa’adin Tsofaffin Takardun Kudi Na Naira

Babban bankin Najeriya ya kara wa’adin canza shekar tsohon kudin Naira. An sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da babban bankin…

Babban bankin Najeriya ya kara wa’adin canza tsohon kudin Naira.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban bankin ya fitar a Yau Lahadi

A cikin sanarwar, gwamnan bankin Godwin Emefiele, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada izinin kara wa’adin zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu.

Ya ce ya zuwa yanzu, CBN ya tara tiriliyan 1.9 sannan ya bar biliyan 900 don cimma nasarar aiwatar da manufofin.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “A Karshe CBN Ya Tsawaita Wa’adin Tsofaffin Takardun Kudi Na Naira”