October 31, 2021

A karon farko shugaban kungiyar Taliban ya bayyana a gaban jama’a

Muhammad Bakir Muhammad


Shugaban kungiyar Taliban Haibatullah Akhundzada ya bayyana a gaban jama’a ya kuma gabatar da jawabi a karon farko, inda ya gabatar da jawabin ga mabiyansa da ke kudancin birnin Afghan na Kandahar.

Shugaba Akhundzada ya kasance shugaban kungiyar ta da kayar baya da rajin kafa gwamnatin musulunci ta Taliban tun shekarar 2016 sai dai kuma ya kasance a boye har bayan nasarar da kungiyar tasa ta samu na juya akalar mulki da shugabanci a kasar ta Afghanistan a watan Agusta da ta gabata.

A yan watannin baya har an fara rade-radin mutuwar sa.
A ranar Asabat ne Akhundzada ya ziyarci madrasa na Darul Ulum don ganawa da sojojin sa, mabiyan sa da kuma daliban sa, kamar yadda Taliban ta sanar.

Wurin taron ya kasance cike da sojoji cikin shirin ko ta kwana, inda aka tsaurara tsaro, sannan babu wani hoto ko bidiyo da ya fito daga zauren wanda ya nuna yadda ganawar ta kasance.

Sai dai akwai wata murya da aka nad’a na kimanin mintuna 10 wanda aka sake shi a shafukan sada zumunta na Taliban.

Akhundzada wanda ake ma lakabi da “Amirul Muminin” ma’ana shugaban muminai ya isar da sako ga mabiyan nasa.

Sai dai bai yawaita magana kan lamarin siyasar ba, sai dai ya yi magana ne kan abinda ya shafi addini da kuma sanyawar albarka ga gwamnatin Taliban.

Daga karshe ya yi addua ga shahidan su na Taliban da kuma sojojin da suka jikkata yayin gwawarmayar.

SHARE:
Labaran Duniya, Rahotanni 0 Replies to “A karon farko shugaban kungiyar Taliban ya bayyana a gaban jama’a”