December 12, 2022

A jiya ne, aka watsa Tokar gawar marigayi Jiang Zemin a cikin teku da ke gabar kogin Yangtze kamar yadda shi da iyalinsa suka bar wasiya.

A jiya ne, aka watsa Tokar gawar marigayi Jiang Zemin a cikin teku da ke gabar kogin Yangtze kamar yadda shi da iyalinsa suka bar wasiya.
Jiang ya rasu ne a birnin Shanghai, ranar 30 ga watan Nuwamba yana da shekaru 96. An kona gawarsa a ranar 5 ga watan Disamba a birnin Beijing.
Bisa amincewar kwamitin kolin JKS, da Cai Qi, mamban zaunannen kwamitin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS, kuma mamba a sakatariyar kwamitin kolin JKS, da sauran jami’ai, da uwargidan Jiang Wang Yeping, da sauran ‘yan uwa ne suka raka tokar Jiang zuwa teku. An yi hakan ta hanya mafi girmama da daraja, don nuna alhini da tunawa da Jiang cikin girmamawa.
An yaba wa marigayi Jiang a matsayin fitaccen shugaba da daukacin jam’iyyarsa, da dukkan sojoji da jama’ar kasar Sin na dukkan kabilu suka amince da shi suke dauka da daraja da martaba matuka, babban mai ra’ayin Markisanci, babban dan juyin juya hali, dan siyasa, masanin dabarun soja, kuma jami’in diflomasiyya, jarumin kwaminisanci da aka dade da yarda da shi kuma fitaccen shugaba da aka yi gwagwarmayar kafa tsarin gurguzu mai sigar kasar Sin.
Shi ne kuma jigon jam’iyyar karni na uku na shugabancin kolin gama gari kuma jagoran da ya kafa ka’idar wakilai uku.
A matsayinsa na dan jari-hujja, Jiang ya bayyana fatansa na watsa tokarsa a cikin kogin Yangtze da teku. Ya sadaukar da rayuwarsa baki daya ga kasarsa da jama’a ba tare da wani gayiyawa ba.
Ban kwana, mai daraja Kwamared Jiang Zemin! Sunansa da nasarorinsa da tunaninsa da halayensa, za su dauwama a tarihi, kuma su kasance har abada a cikin zukatan jama’a.

©cri (Ibrahim Yaya)

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “A jiya ne, aka watsa Tokar gawar marigayi Jiang Zemin a cikin teku da ke gabar kogin Yangtze kamar yadda shi da iyalinsa suka bar wasiya.”