A Cikin Sa’o’i 24, Yan Gwagwarmaya A Palasdinu Sun Kai Hare-hare Sau 15

Majiyar da take kula da tattara bayanai ta Palasdinawa ta ce; A cikin sa’aoi 24 da suka wuce, palasdinawa ‘yan gwagwarmaya sun kai hare-hare akan manufofin ‘yan sahayoniya har sau 15.
Majiyar ta cigaba da cewa; Yan share wuri zauna 4 sun jikkata, a lokacin da mutane garin Jaurish suke kare garin nasu daga harin da aka kai musu.
Har ila yau, an yi taho mu gama har a wurare 6 a cikin yammacin Kogin Jordan a tsakanin ‘yan share wuri zauna da samarin Palasdinawa. Daga cikin wuraren da akwai Sansanin yan hijira na Sh’adhaf, da garin Nabi-Saleh, da Ra’as Shumar da ke Tul-Karam.
Daga farkon wannan shekara ta 2023 zuwa yaznu, a kalla Palasdinawa 13 ne su