January 25, 2023

a a rufe kasuwanci a Kebbi saboda matsalar sauyin kuɗi

‘Yan kasuwa a Birnin Kebbi da ke arewacin Najeriya sun yanke shawarar rufe harkokin kasuwancinsu saboda ƙarancin sabbin kuɗi, wanda hakan ya sa harkokin kasuwancin fuskantar koma baya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwa a Jihar Kebbi Alhaji Umar Dangura Gwadangwaji, ne ya bayyana hakan, yana cewa ‘yan kasuwa na ta ƙoƙarin samun sabbin kuɗin daga bankuna amma hakan ya ci tura.

“In muka ci gaba da karɓar kuɗi daga hannun kwastoma, to wanne banki ne zai karɓi kuɗaɗen kafin a daina amfani da su,” in ji shi.

A cewar jaridar masu hayar mota da masu sayar da kayayyaki a gefen tituna a ranar Talata sun daina karɓar tsofaffin kudi daga kwastoma, saboda bankuna da masu POS basu da sabbin kuɗin suma.

©BBC

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “a a rufe kasuwanci a Kebbi saboda matsalar sauyin kuɗi”