July 20, 2023

Tambayoyi da amsoshi akan zaman juyayin Aba Abdullahi a.s Daidai da fatawar Sayyedul ka,id Dz

T: Muna son sanin siffofin karbabben juyayin zaman makokin Imam Husaini (a.s) a wajen Ahlulbaiti (a.s)?

Amsa: Yayin amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa juyayi yana da wasu abubuwan lura guda biyu: na farko shi ne abin da (juyayin) ya kumsa da kuma abubuwan da ake fadi a cikinsa. Na biyu kuma shi ne salon da ake gudanar da juyayin. Dangane da abin da ya kumsa, wajibi ne abin da ake fadi ya kasance ba abubuwan da aka haramta ba ne, ba wadanda suka saba wa shari’a ba ne. Wato kada a fadi karya, kada a fadi abubuwan wuce gona da iri (guluwi), kada ya zamanto abin da zai janyo zubar da mutumcin mazhaba, kada ya zamanto abin da zai zubar da mutumci da rage matsayin Imam Husain (a.s) da sauran Ma’asumai (a.s). Haka nan kuma kada ya zamanto abin da zai rage matsayi da mutumcin su kansu muminai masu juyayin. Wato wajibi ne abin da za a fadi ya zamanto akwai tabbas cikinsa, bai saba wa mazhabar Ahlulbaiti (a.s) ba, bai saba wa matsayin Ahlulbaiti da dai sauran abubuwa makamantan hakan.

Dangane da salon juyayin kuwa; to shi ma dai da farko kar ya zamanto akwai ayyuka na haram a cikinsa. A matsayin misali kida na haram da makamantan hakan. Haka nan kuma kada ya zamanto abin da zai janyo cin mutumcin mazhabar. Wato kada mu yi abin da zai zamanto wani makami a hannun makiya ta yadda za su sami wani abu na yada bakar farfaganda a kan mazhabar Ahlulbaiti da mabiyansu.

A takaice ana iya cewa wadannan su ne siffofin da ya wajaba a ce duk wani juyayi abin karbuwa a wajen Ahlulbaiti (a.s) yana da su.

T: Shin akwai matsala cikin cin abincin da ake rabawa a ranakun Ashura da mutum ba shi da tabbaci kan halascinsa? Ina son amsa ne ta bangaren hukunci na fikihu da kuma bangaren kyawawan halaye. Sannan kuma mene ne hukuncin cin abincin bakancen da mutumin da ba ya fitar da Khumusi ya raba?

Amsa: Dangane da cin abincin da mutum ba shi da yakinin haramcinsa, a matsayin misali wasu suka kawo wa masu juyayi da zaman makoki abinci ko kuma wani mutumin da kuke da yakinin ba ya fitar da Khumusi ya kawo muku abincin bakance, to ra’ayin Jagora a nan shi ne cewa babu matsala cikin cin wannan abincin, don kuwa ba ku da yakinin haramcinsa ko kuma haduwarsa da haram. Wato ba ku da yakinin cewa wannan abincin na haram ne, ba ku da yakinin cewa Khumusi ya hau kansa.

To amma a mahanga ta kyawawan halaye – kamar yadda aka tambaya – wasu suna cewa idan har akwai kudin Khumusi a cikin hakan, lalle yana iya yin mummunan tasiri. Idan har mutum zai iya yin ihtiyadi, lalle yana da kyau. Wato idan dai bai zama dole ba, kada mutum ya ci. Ko kuma ga misali idan har ana shakkun ko Khumusi ya hau kan kudin, to ku da kanku ku fitar da Khumusinsa ko kuma idan ya zamanto kana da shakku kan haramcinsa. A matsayin misali kudi ne da ba a san me shi ba, to sai a cire shi a matsayin mayar da abin da aka kwata ko aka same shi ta hanyar haramun sannan ba a tantance mai shi ba; duk kuwa da cewa hakan ba wajibi ba ne. A hukunci na farko mun fadi cewa babu matsala cikin cin abincin da ba a da yakinin haramcinsa ko kuma haduwarsa da haramun. A mahangar fikihu dai ba haramun ba ne. Amma idan har mutum yana son ya zamanto daga cikin waliyan Allah, to yana da kyau ya nesanci hakan.

 

 

SHARE:
Mas'alolin Fiqihu 0 Replies to “Tambayoyi da amsoshi akan zaman juyayin Aba Abdullahi a.s Daidai da fatawar Sayyedul ka,id Dz”