June 5, 2023

Amurka da Saudiyya sun sake sabon yunkuri na yin sulhu tsakanin janar-janar da ke rikici a Sudan

 

Amurka da Saudiyya sun sake sabon yunkuri na yin sulhu tsakanin janar-janar da ke rikici a Sudan a daidai lokacin da aka shiga mako na takwas na rikici a kasar.

Masu shiga tsakani na kasashen waje sun yi kira ga “bangarorin biyu su amince su aiwatar da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta, da zummar samar da wata hanya ta magance rikicin”, kamar yadda Riyadh ta bayyana ranar Lahadi.

Rahotanni na cewa har yanzu ana ci gaba da gwabza fada a kasar.

Alkaluma sun nuna cewa an kashe fiye da mutum 1,800 a rikicin na Sudan da ya barke a ranar 15 ga watan Afrilu.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Amurka da Saudiyya sun sake sabon yunkuri na yin sulhu tsakanin janar-janar da ke rikici a Sudan”