June 1, 2023

​Iran Da Iraki Sun Cimma Yarjiyar Bude Kofofin Shiga Kasashen 2 Har 6 Ga Masu Ziyarar 40 Na Imam Hussain(a)

Ministan harkokin cikin gida na kasar Iran Ahmad Wahdi tare da tokwaransa na kasar Iran Abdul-Amir Al-shammari sun cimma yarjeniyar samarda kofofin shiga da fita tsakanin kasashen biyu har guda 6 a kwanakin 40 na Imam Hussain (a) mai zuwa, sannan za’a bar kofar shiga da fita ta Khosravi a bude na dare da rana na tsawon kwanakin.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministocin biyu suna fadar haka a jiya Laraba bayan ganawa a ma’aikatar cikin gida a nan birnin Tehran.

Labarin ya kara da cewa bangarorin biyu sun cimma matsaya kan al-amuran tsaro da kuma fayyace kan iyakar kasashen biyu na kan duwatsu, ruwa da kuma kan tdu.

Har’ila yau sun amince su yi musayar bayanai a tsakaninsu dangane da samu safarar miyagun kwayoyi da gungun masu aikata laifuffuka.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Iran Da Iraki Sun Cimma Yarjiyar Bude Kofofin Shiga Kasashen 2 Har 6 Ga Masu Ziyarar 40 Na Imam Hussain(a)”