Babban bankin Najeriya CBN ta rage darajar kudaden ksar Naira daga naira 461.6 kan ko wace dalar Amurka zuwa naira 630.
Jaridar Daily Trunst ta Najeriya ta bayyana cewa babban bankin ya dau wannan matakin ne bayan jawabin sabon shugaban kasa na farko a taron rantsar da shi a ranar 29 ga watan mayun da ya gabata. Da kuma bukatar shirinsa na daidaita farashin dalar a babban bankin da kuma na kasuwar cangi na yan kasuwa.
Bayan wannan sanarwan dai farashin dalar Amurka a kasuwar canji ya ragu daga naira N750 zuwa 745 a ranar tarlatan da ta gabata a biranen Abuja da kuma Kano
Har’ila yau a jiya laraba ce kamfanin man fetur na kasa NNPCL ya bada sanarwan kara farashin tatacce man fetur a duk fadin kasar daga naira
Jaridar Premium times ta bayyana cewa kamfanin ya fitar da wata sanarwa a rubuce a jiya Laraba inda a ciki ya bayyana karin farashin man fetur daga N194 kan ko wace lita zuwa N537 a Abuja.
Labarin ya kara da cewa farashin man a sauran jihohin kasar sun kama daga N515 zuwa N537. Wannan ma ya zo ne bayan da sabon shugaban kasar ya bada sanarwan cire tallafin man fetur wanda gwamnatin tarayyar da ta shude take bayarwa kafin ta sauka.