May 13, 2023

Jaridar Leadership ta Najeriya ta nakalto ministan harkokin cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola yana fadar haka a jiya a lokacinda yake kaddamar da babban cibiyar gyaran hali ta kasa a birnin Owerri na jihar Imo.

Minisya ya kara da cewa kashi 90% na fursinoni a kasar sun shafi jihohin kasar ne don haka daga shekara mai zuwa gwamnatocin jihohi ne zasu dauki nauyin ciyarda fursinoninsu. Har’ila yau ministan yana fadar haka ne a dai dai lokacinda gwamnatin tarayyar ta bada sanarwar ware naira biliyon N22.4 don ciyar da fursinoni a cikin kasasfin kudin wannan shekara.

Ministan ya kara da cewa gwamnatin shugaba buhari ta gabatar da sauye sauye da dama a cikin al-amuran gidajen yari da kuma shari’ar kasar, saboda matsaloli da dama da suke fuskantarsu. Daga ciki kasha 80% na fursinonin masu jiragen shari’a ne, sannan wasunsu sun wace mafi yawan shekarun da za’a tsare mutum ko da a yanke masa hukunci.

Wanda ya nuna cewa dole a sake lale kan yadda harkokin shari’a suke tafiya a kasar don rage zaluntar da akewa da dama daga cikin fursinoni a kasar.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “”