May 10, 2023

Nijar: Fiye Da Mutane 13,000 Ne Su Ka Gudu Daga Gundumar Tillaberi Da Ake Fama Da Rikici

 

A jiya Talata ne Radiyon “Voix Du Sahel” ya bayar da labarin cewa; Fiye da mutane 13,000 ne mata da kananan yara su ka gudo daga wani yanki na gundumar Tillaberi da ake fada a tsakanin mazauna yakin da masu dauke da makamai.

Radiyon ya kuma cigaba da cewa, masu dauke da makaman da su ka kai hari a Ayoru sun tilastawa mutanen yin hijira zuwa inda za su sami aminci a yankin da yake da nisan kilo mitan 200 daga babban birnin kasar Niamey.

Mutanen yankunan Dessa da Kandadji inda ake da madastar ruwa ta samar da wutar lantarki ta farko a kasar, suna fuskantar cin zarafi daga masu dauke da makamai.

A garin Dessa mutane hudu ne su ka kwanta dama a harin daren Asabar zuwa Lahadi.

“Yan majalisar kasar ta Nijar da su ka fito daga gundumar ta Tillaberi sun kai ziyara a yankuna uku da rikicin ya rutsa da su, suna nuna goyon bayansu ga mutane da rikicin ya ritsa da su.

Wani dan jarida ya bayyana cewa, masu jabun jihadi a yankin ne suke kashe fararen hula da kuma sace musu dabbobi.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Nijar: Fiye Da Mutane 13,000 Ne Su Ka Gudu Daga Gundumar Tillaberi Da Ake Fama Da Rikici”