April 28, 2023

 

Dubban mutanen kasar Sudan suna kara kwarara zuwa kasar Masar saboda kaucewa yakin da ke faruwa tsakanin sojojin kasar.

Shafin labarai na yanar Gizo Afirka News ya bayyana cewa motoci dauke da yan gudun hijira a mashigar kasar Masar kan iyaka da kasar Sudan da ake kira Arqin suna layin jiran izinin shiga kasar ta masar.

Jami’am ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ta bada sanrwan cewa ya zuwa jiya Alhamis mutane kimanu 14,000 suka tsallaka kan iyakar zuwa cikin masar, tun bayan fara yakin.

Labarin ya kara da cewa daga cikinsu akwai yan kasar ta Sudan da kuma mutane kimani 2000 na wasu kasashen duniya da suke zaune a kasar ta sudan. Sun hada da jami’an diblomasiyya, ma’aikatan kungiyoyin kasa da kasa da sauarnsu.

Ya zuwa yanzu dai an kashe mutane fiye da 500 sannan wasu fiye da 4000 suka ji rauni. Kuma babu alamun bangaroin da sike fafatawa kasar zasu daina yaki nan kusa.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “”