April 12, 2023

MDD ta bukaci a samar da tallafin Biliyan 2,6 ga somaliya.

 

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a samar da gagarimin tallafin kasa da kasa ga Somaliya.

“Ina kira ga masu hannu da shuni, kuma ina kira ga kasashen duniya da su kara kaimi wajen bayar da tallafin gaggawa ga shirin ba da agajin jin kai na shekarar 2023 wanda a halin yanzu kashi 15% ne kawai aka samu,” in ji Guterres.

MDD, Ta ce tana Bukatar A Samar Da Tallafin Dala Biliyan 2,6 Ga Somaliya

Mista Guteress, ya bayyana hakan ne a ziyarar da ya kai kasar da ke fama da tashe tashen hankula a yankin kahon Afirka a ranar Talata.

Kimanin rabin al’ummar kasar za su bukaci agajin jin kai a bana, inda mutane miliyan 8.3 ke fama da fari a cewar Majalisar Dinkin Duniya

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “MDD ta bukaci a samar da tallafin Biliyan 2,6 ga somaliya.”