April 9, 2023

 

Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ko (IRGC) ya bada sanarwan cewa daya daga cikin su mai suna Milad Heidari ya yi shahada a kasar Siyar a jiya Jumma’a sanadiyyar hare-haren ta’adanci na jiragen yakin HKI a kan birnin Damascus babban birnin kasar Siriya.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa Milad Haidari yana daga cikin sojoji masu bada shawara ga gwamantin kasar Syriya, kuma jiragen yakin HKI sun kashe shi ne a lokacinda yake bakin aikinsa.

Rundunar ta sha alwashin ramawa da kuma daukar fansar shahidanta kan HKI, labarin ya kara da cewa: Jinin shahidammu ba zasu tafi a banza ba. Labarin ya bayyana cewa za’a bayyana lokacin jana’izarsa nan gaba.

Daga karshe dakarun sun yi allawadai da shirun da kasashen duniya mambobi a MDD suka yi dangane da hare-haren ta’addancin da sojojin HKI suke kai kasar Siriya.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “”