Iran : Jagora Ya Nemi Kasashe Masu Son Adalci A Duniya Su Hada Kansu.

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya yi kira ga kasashen duniya wadanda suke son adalci susan junansu su kuma hada kansu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jagoran yana fadar haka a wani jawabin da ya aikawa taron al-aduna na hadin giwa tsakanin kasashen Iran da Venezuela a birnin Carakas babban birnin kasar Venezuela.
Labarin ya kara da cewa sakon jagoran har’ila yau ya zo a dai-dai lokacinda aka kaddamar da wani littafi mai suna “Daki mai lamba 14’ wanda aka tarjama zuwa harshen espaniyanci, wanda kuma yake magana kan tarihin gwagwarmayan Imam Sayyid Aliyul Khamanie da sarakunan Iran kafin nasarar juyin juya halin musulunci a kasar a shekara 1979.
Jagoran ya bayyana cewa wannan littafin dan kadan ne daga rayuwarsa ta gwagwarmaya da sarakunan kasar Iran kafin nasara, ya kuma kara da cewa
“yana da kyau da mu da mutane masu son adalci daga kasashen da suke magana da harshen espaniyanci mu san juna kuma don tafiya tare yafi dacewa da samun nasara”.
Kafin haka dai an fassara littafin Daki na 14 zuwa harshen larabaci daga harshensa na asali wato farisanci.