February 13, 2023

Rundunar sojojin kasar Iraki ta bayyana a jiya Lahadi cewa, sojojin saman kasar sun kai harin sama a lardin Diyala, inda suka kashe dakarun IS guda bakwai.
A jiya Lahadi, kakakin babban kwamandan rundunar sojojin kasar Yahia Rasoul, ya sanar da cewa, sojojin kasar sun kai wa maboyar dakarun IS a tudun Himreen dake arewacin lardin Diyala hari da jirgin saman yaki, da taimakon hukumar leken asiri, inda suka kashe mayakan kungiyar bakwai, ciki har da madugun ta.
A watan Disamban shekarar 2017, Iraki ta sanar da cewa, ta cimma nasarar dakile kungiyar IS, to sai dai daga baya, sauran wasu dakarun kungiyar sun ci gaba da kai hare-hare a kauyukan kasar, ko wuraren dake kan iyakar kasar da Syria.
A cikin yan watannin da suka gabata, sojojin Iraki sun kara daukar matakan soja a kauyukan kasar, domin ganin bayan kungiyar daga duk fannoni.

 

©CRI Hausa(Jamila)

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “”