February 13, 2023

Sabbin alkaluman da hukumar kula da iftila’i da agajin gaggawa ta kasar Turkiyya ta fitar a jiya Lahadi sun shaida cewa, sama da gine-gine dubu 20 sun rushe, sakamakon girgizar kasa da ta afkawa kudancin kasar a ranar 6 ga watan nan, lamarin da ya jawo shakku kan ingancin gine-ginen.
©CRI Hausa (Lubabatu)