January 27, 2023

Rundunar ‘yan sandan Najeriya, ta ce a kalla mutane 27 sun rasu, sakamakon wata fashewa da ta auku a jihar Nasarawa ta yankin tsakiyar Najeriya.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ramhan Nansel, ya ce fashewar ta auku ne a daren ranar Talata, kuma ya zuwa yau Alhamis, an gano gawawwakin mutane 27 daga wurin da lamarin ya auku. Kaza lika jami’an tsaro na ci gaba da bincike domin tantance ko akwai karin wasu mutane da lamarin ya rutsa da su.
Bugu da kari, jami’in ya ce dukkanin wadanda fashewar ta shafa makiyaya ne dake zaune a Rukubi, wani yanki dake kan iyakar jihar ta Nasarawa da jihar Benue.
A jiya Laraba, yayin zantawar sa da kafofin watsa labarai a birnin Lafia fadar mulkin jihar Nasarawa, gwamnan jihar Abdullahi Sule, ya bayyana matukar takaicin aukuwar lamarin, yana mai shan alwashin tabbatar da an cafke wadanda suka kitsa fashewar, tare da gurfanar da su gaban shari’a.

 

©(Saminu Alhassan)

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “”