January 23, 2023

Wani daga cikin jagororin kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Jiahdul-Islami, Ahmad Mudallal ne ya kira yi gwamnatin kasar Sweden da ta nemi gafarar al’ummar musulmi akan abinda aka aikata na kona alkur’ani a cikin kasarta.

Mudallal ya fadawa kamfanin dillancin labarun Palasdinawa cewa “ Abinda ya faru a Sweden din na nuna kiyayya ga musulmi da tsokanarsu ,ya nuna cewa kasar ba ta da wani wayewa ko cigaba.”

Jagoran na kungiyar Jihadul-Islami ya bukaci ganin gwmanatin Sweden ta hukunta wanda ya aikata wannan danyen laifi akan al’ummar musulmi.

Har ila yau mudallal ya kira yi kasashen musulmi da na larabawa da su yanke alakar diplomasiyya da kasar ta Sweden, su kori dukkanin jakadunta da suke a cikin kasashensu.

Gwamantin kasar ta Sweden ta kyale wani dan siyasar kasar Denmark mai bakar adawa da musulunci ya shiga cikin kasar sannan ya yi bikin kona alkur’ani maigirma a gaban ofishin jakadancin Turkiya.

Kasashen musulmi dai suna cigaba da mayar da martani akan abinda ya faru tare da bayyana shi a matsayin tsonaka.

Tun daga shekarar 2017 ma dai dan siyasar na kasar Denmark Rasmus Paludan yake yin wannan irin wautar ta kona alkur’ani mai girma a can kasarsa

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “”