January 15, 2023

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci daukar matakan gaggawa don ceto yara fiye da miliyan 30 da ke fuskantar barazanar cutar yunwa a kasashe 15 da ke fama da matsananciyar yunwa ciki har da Najeriya.

Sanarwar wadda sassan lafiya da abinci da kuma kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya 5 suka fitar sun yi gargadin cewa matukar ba a dauki matakan da suka kamata ba, ko shakka babu yaran fiye da miliyan 30 za su fuskanci cutar yunwa sakamakon rashin abinci mai gina jiki.

Sanarwar ta Majalisar Dinkin Duniya da ke wannan gargadi ta zayyano kasashen da za su fuskanci wannan matsala ciki har da Afghanistan da Burkina Faso da Chadi da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo baya ga Habasha da Haiti da Kenya da kuma Madagascar sai kasashen Mali, Nijar, Najeriya da Somalia da Sudan ta kudu kana Sudan da Yemen.

Sassan na Majalisar 5 da suka kunshi hukumar abinci ta duniya FAO da mai kula da bakin haure UNHCR da kuma asusun tallafawa kananan yara na UNICEF da WHO baya ga shirin samar da abinci na duniya WFP sun ce wajibi ne a hada hannu don hana faruwar wannan annoba da ke tunkaro Duniya.

A cewar sanarwar sassan 5 cutar ta yunwa ko kuma rashin abincin mai gina jiki ga kananan yara na sahun cutukan da ke haddasa asarar rayukan miliyoyin yara kowacce shekara musamman a matalautan kasashe ko kuma wadanda yaki ko matsalar tsaro ta daidaita.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “”