January 12, 2023

​Masar: An Kama Wasu Mutane Da Suke Shirin Sace Gunkin Fir’ana

Mahukuntan Masar sun sanar da kame wasu mutane 3 da ke yunkurin sace gunkin Fir’auna da aka fi sani da Pharaoh Ramses na biyu, mutum-mutumin da ke da nauyin tan 10.

Sanarwar da Ofishin mai shigar da kara na Masar ya fitar ya ce mutanen 3 sun yi amfani da wani katon injin daukar kaya don sace gunkin wanda ke kudancin birnin Aswan mai tazarar kilomita 675 da birnin Cairo fadar gwamnati.

Tuni dai ofishin ya bude shafin bincike na kwanaki 3 kan mutanen don tabbatar da manufarsu game da yunkurin sace gunkin na Fir’auna mai matukar tarihi.

Rundunar ‘yan sandan kasar ta tabbatar da kame mutanen 3 dauke da tarin kayakin haka da kuma babban injin daukar kaya masu nauyi, wanda ken una matukar bincike ya kammala akansu kai tsaye za su gurfana gaban Kotu don amsa laifinsu.

Baya ga mutanen 3 Ofishin mai shigar da kara na Masar ya kuma bukaci lalubo wadanda ke da hannu a yunkurin don hukunta su.

Fir’auna na II ko kuma Pharaoh Ramses na biyu na sahun Fir’aunonin da Masar ta yi a tarihi wanda ya yi mulki a karni na 19 ya suna ne saboda jarumtarsa da kuma kasancewarsa mayaki na gaske.

 

©Hausa TV.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Masar: An Kama Wasu Mutane Da Suke Shirin Sace Gunkin Fir’ana”