November 28, 2022

Da ƊUMI-ƊUMI: Gwamnan Osun, Adeleke ya sauke sarakuna 3

Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya sauke wasu sarakuna uku da tsohon gwamna, Adegboyega Oyetola ya naɗa.

Tsohon Gwamna Oyetola ya naɗa sarakuna da dama makonni kadan kafin ya mika mulki ga Adeleke, wadanda su ka hada da Akirun na Ikirun, Oba Yinusa Akadiri, Aree na Iree, Oba Ademola Oluponle da Oba Adegboyega Famodun.

Tsohon gwamnan ya kuma amince da nadin sakatarorin dindindin guda 30 a ma’aikatu daban-daban.

Sai dai Adeleke, a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Olawale Rasheed, kimanin awanni 24 da rantsar da shi, ya bayyana tuɓe rawunnan Sarakunan Akirun na Akirun, Aree na Iree da kuma Owa na Igbajo har sai sakamakon kwamitin bincike ya sake duba nade-naden da aka yi da kuma nada mukamai da aka yi.

Sanarwar ta ce, a safiyar yau ne aka sanya hannu kan dokar zartaswa guda shida da gwamnan ya bayar wadanda suka shafi sauya mukaman sarakuna, nadawa da sanya ma’aikatan gwamnati, daukar ma’aikata da kuma daskarar da asusun gwamnati da kuma fara aiki nan take.

“Dukkan nade-naden sarakunan gargajiya da gwamnatin jihar Osun ta yi bayan ranar 17 ga watan Yuli, 2022, an ba da umarnin sake duba su don tabbatar da bin ka’idojin da suka dace na ayyana sarauta da dokokin kasa, al’ada da su ka shafi irin wadannan masarautun.

“Dangane da batun Ikirun, Iree da Igbajo, don gudun kada a samu tabarbarewar doka da oda, an dage nadin Akinrun na Ikinrun, Aree na Ire da Owa na Igbajo. Daga nan kuma, fadar Akinrun na Ikirun, Aree na Iree da Owa na Igbajo, su kasance babu kowa a ciki, yayin da aka umarci jami’an tsaro da su kula da fadojin,”.

©Daily Nigeria.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “”