October 8, 2021

Falalar Salatin Annabi A Ranar Juma’a

Muhammad Awwal Bauchi


“عن حماد بن عثمان ، أنّهُ سأل أبا عبد الله (عليه السلام) قال : أخبرنا عن أفضل الأعمال يوم الجمعة ؟ فقال : الصلاة على محمد و آل محمد مائة مرة بعد العصر ، و ما زادت فهو أفضل”

Daga Hammad bn Usman, cewa ya tambayi Imam Sadiq (a.s) cewa: Ka ba mu labarin mafi girma da daukakar ayyukan ranar Juma’a. Sai ya ce: “Salati ga Annabi Muhammadu (s) da Alayensa sau dari bayan (sallar) La’asar, abin da ya karu kan hakan kuwa shi ya fi”.

A wani hadisin kuma an tambaye shi (a.s) kan yadda za a yi salatin sai ya ce ka ce:

اَللّهمَّ صَلِّ على محمّدٍ وآلِ محمّد، وعجِّلْ فَرَجَهم

Allah Ya sanya mu daga cikin masu yawaita Salati da Annabi da Alayensa (a.s).

Barkanmu da Juma’a, Allah Ya maimaita mana

SHARE:
Tarbiyyan Yara 0 Replies to “Falalar Salatin Annabi A Ranar Juma’a”