September 23, 2021

Yakin Basra Ko Kuma Yakin Jamal

Daga Muhammad Awwal Bauchi


Matsayar da Imam Ali (a.s) ya dauka ta daidaita tsakanin al’ummar musulmi ba tare da wani banbanci ba, sannan kuma da hana wasu manyan mutane diban dukiyar al’umma ba ta yi wa Dalhat da Zubair dadi ba, wannan ya sa suka fara shirye-shiryen kalubalantar Imam (a.s), da tunzura Musulmi a kansa; wannan ne ya haifar da fitinar da ta yi sanadiyyar matsananciyar hasara ga al’umma; yayin da suka bukaci da A’ishah ‘yar Abubakar matar Annabi kan cewa ta fito tare da su zuwa Basra, don ta jagoranci rundunar fito-na-fito da yakan Imam Ali (a.s).
A Basra kuwa, Imam (a.s) ya ci gaba da gabatar da nasihohi don ganin ba a zubar da jini ba, inda ya aikawa ‘yan hamayyan da dan sako ya kira su zuwa ga sulhu, amma abin ya ci tura. Imam da kan shi ya hadu da Zubairu, ya kuma tuna masa da wasu al’amurra da suka faru gare su a lokacin Annabi (s.a.w.a); daga ciki har da fadar Manzo (s.a.w.a) ga Zubairu din cewa:

“Wata rana za ka fito yakarsa -wato Imam Ali- alhali kana mai zaluntarsa.” Sai Zubairu ya ce: “Wannan haka ne wallahi! Sai dai ni na mance wannan ne, bayan ka tunatar da ni kuwa lallai zan koma(1).

Har Zubairu ya kulla azamar janyewa, amma sai dansa Abdullahi ya siffanta shi da cewa in har janye shi matsoraci ne.

A bangare guda kuma, Ummul Muminina A’isha, matar Manzon Allah kana kuma ‘yar halifa Abubakar, tana garin Makka don ziyara kwatsam sai ga labari ya zo mata cewa an kashe halifa Usman bn Affan. Jin wannan labari dai ya yi wa A’isha dadi don kuwa tana daga cikin wadanda suke ganin Usman ya kauce wa hanya, to amma lokacin da ta ji al’umma sun zabi Ali a matsayin halifa sai hankalinta ya tashi ta yi fushin gaske sai ta fara tunanin yadda za ta bullo wa lamarin. Don haka sai ta koma tana cewa an kashe Usman cikin zalunci, kuma lalle za ta dau fansar jininsa. A nan tana nufin Imam Ali (a.s) na da hannu cikin kashe Usman don haka za ta dau fansa a kansa.

Don haka sai ta hada kai da Talha da Zubairu wadanda da man suna neman hanyar da za su kawo cikas wa Ali (a.s) da cutar da shi. Talha da Zubairu dai suna a matsayin surukai ne wa A’isha, saboda karamar kanwarta tana auren Talha, shi kuma Zubairu yana auren yayarta. Don haka sai ta fara kulle-kulle da tara sojojin da za su taimaka mata wajen cimma wannan buri nata, inda ta sami gagarumar gudummawa da goyon baya daga Banu Umayyawa, wato kabilar su Usman din, a gefe guda kuma gwamnonin Usman da Ali (a.s) ya cire su ma suka goya mata baya. Daga cikin wadannan gwamnoni har da gwamnan Yemen, wanda ya kwashi dukkan dukiyar da take Baitul Mali ya nufi Makka da ita bayan da aka tube shi ya mika wa A’isha.

Su ma a nasu bangaren Talha da Zubair, (wadanda da farko sun yi bai’a wa Ali (a.s) bayan sun hada kai da A’ishan sai suka ci gaba da tara dakaru da ba da cin hancin wa wasu don su shigo cikinsu, ta haka suka sami wani adadi mai yawa na daga larabawa musamman ma dai wadanda Ali (a.s) ya kashe musu iyaye da ‘yan’uwa a lokacin da yake yaki don kare Musulunci karkashin tutar Manzon Allah (s).

Bayan an gama shirye-shiryen yaki, sai Ummul Muminina A’isha da sojojinta suka nufi Basra. Kafin ta fita dai sai da ta bukaci Ummu Salma, madaukakiyar matar Manzon Allah (s), da ta raka ta, to amma ina ta ki yarda da hakan tana mai tunasar da ita (A’isha) gargadin da Manzo (s) ya yi musu (matayensa) kan cewa karnukan Haw’ab za su yi ihu wa daya daga cikinsu, kuma nan ne kahon fitina zai tsiro (wato za ta kasance mai ta da wutar fitina)(2). Wannan nasiha ta Ummu Salma ta yi tasirin gaske a zuciyar A’isha har ta fara tunanin ta janye daga wannan nufi nata, to sai dai kuma Abdullah bn Zubair, dan agolanta, ya sawo kanta kan kada ta canza wannan matsaya tata, inda ta yarda ta ci gaba.

Daga nan sai ta hau rakumarta, ta fito daga Makka alhali tana jagorantar sojoji kimanin 1000, sannan kuma ta ci gaba da samun wasu a hanya har dakarun nata suka kai kimanin 3000.

 

Zamu cigaba…

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “Yakin Basra Ko Kuma Yakin Jamal”