August 28, 2021

Laifin Kisa: An Yafewa Wata Mata Da Ta Kashe Mijin ta A Kano

Daga Muhammad Bakir Muhammad

Laifin Kisa: An Yafewa Wata Mata Da Ta Kashe Mijin ta.

Daga Muhammad Bakir Muhammad

Wata mata mai suna Rahma Husain ta samu yafiyan hukuma bisa laifin da ake tuhumar ta da shi a kisan mijinta shekaru 7 da suka gabata.

Al’amarin dai ya faru ne tun shekaru 7 da suka gabata; a shekarar 2014, a sain nan tana ‘yar shekara 16 aka gurfanar da ita gaban wata kotu a jihar kano inda ake tuhumar ta da laifin kisan mijinta a unguwar Darmanawa ta karamar hukumar Tarauni, a yayin da basu fi mako guda da aure ba.

Sai dai kuma biyo bayan zaman kotu a shekarar 2018 Mai shari’a R. A Sadik ya bada umarnin ci gaba da tsare ta karkashin ikon gwamnan jiha sakamakon ta aikata laifin ne tana ‘yar shekaru 16 kawai, haka zalika tayi hakan bisa auren dole da aka yi mata da mijin ba bisa yardarta ba.

Bayan shekaru 7 yau ta samu yafiyar hukuma, hakan kuwa ya biyo bayan yafiyan da wakilan gwamnatin tarayya kan lamarin gidan gyaran hali suka kaddamar na mutum 31 wanda ta kasance daya daga cikin wadan da akayi ma gafara; a tare da ita akwai wasu mutane 30 daga sauran gidajen gyaran hali na jihar.

A hirar mai Magana da yawun hukumar gyaran hali ta jihar kano, Musbahu Kofar-Nassarawa yayi bayani kasan sakin na ta haka kuma cikin bayanin ya shawarci gwamnan jihar Kano Dr, Abdullahi Ganduje kan ya duba lamarin laifin na ta da kuma dalilin da ya sabbaba hakan a matsayin sa na mai ruwa-da-tsaki kan lamarin sakin nata, haka kuma ya roki gwamnan da ya yafe mata.

Bayan sakin na ta, Rahma cikin hawaye ta bayyana murnar ta da godiyan ta ga gwamnan, hukumar kula da gyaran hali da kuma wakilan na musamman na tabbatar da sakin nata.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Laifin Kisa: An Yafewa Wata Mata Da Ta Kashe Mijin ta A Kano”