March 22, 2024

Falasdinawa sunyi sallan juma,a a masallacin qudus.

Dubban Falasdinawa masu ibada ne suka kama hanyarsu ta zuwa masallacin Al-Aqsa domin gudanar da sallar Juma’a ta biyu na watan Ramadan, duk kuwa da hani da hare-haren da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai musu.

Tun da farko wakilin Al Mayadeen a Palastinu da ke mamaye ya ruwaito cewa IOF na cikin shirin ko-ta-kwana yayin da masu ibada ke kan hanyarsu ta zuwa Al-Aqsa domin gudanar da sallar Juma’a.

Sojojin Isra’ila sun kuma sanya takunkumi mai tsauri kan Falasdinawa da suke tafiya zuwa al-Quds da suka mamaye daga gabar yammacin kogin Jordan don yin addu’a a al-Aqsa.

Kazalika, majiyoyin cikin gida sun bayyana cewa, IOF din sun karfafa kasancewarsu a shingayen binciken sojoji dake kan hanyar zuwa al-Quds, tare da duba katunan tantance Palasdinawa, tare da hana daruruwan mutane shiga.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Falasdinawa sunyi sallan juma,a a masallacin qudus.”