January 17, 2024

Fatima Yar Ma,aikin Allah s.a.w.a Daya Tilo

Sunanta: Fadima.
Sunan mahaifinta: Muhammad xan Abdullahi (s.a.w).
Sunan mahaifiyarta: Khadijatu ‘yar Khuwailidi.
Sunan mijinta: Aliyu xan Abi Dalib (a.s).
Sunayen ‘ya’yanta:
Imam Hasan (a.s).
Imam Husaini (a.s)
Zainab (a.s).
Ummu Kulsum
HAIHUWARTA
An haifi nana Fadima (a.s) a ranar (20) ga watan Jimada Sani bayan shekaru biyar da aiko manzon Allah (s.a.w) a garin Makka.
SUNAYENTA

Wannan baiwa ta Allah tana da sunaye masu yawa, amma zan ambaci guda tara da suka zo a hadisin imam Sadiq (a.s), kuma kowane suna yana da ma’anar da yake xauke da ita. Ga sunayen kamar haka:
(1) Fatima (2) Siddiqa (3) Mubaraka
(4) Xahira (5) Zakiyya (6) Radiya
(7) Mardiyya (8) Muhaddasa (9) Zahra’u

MA’ANONIN WASU DAGA CIKIN SUNAYEN NATA

(1) FATIMA: Akwai ruwayoyi da dama da suka faxi dalilin da ya sa aka ambace ta da wannan suna, daga cikinsu akwai ruwayar da ta zo a cikin littafin: Yanabi’ulmawadda na malam Qanduzi, da littafin: Nurul’absar na malam Shabalanji daga Abuhuraira daga manzon Allah (s.a.w), ya ce: “An ambaci ‘yata da sunan Faxima ne saboda Allah ya kare ta da zuriyarta da masoyanta daga wuta”.
عن أبي هريرة عن رسول الله (ص) أنه قال: (إنما سميت إبنتي فاطمة لأن الله فطمها وذريتها ومحبيها عن النار).
(2) SIDDIQA: Ma’anar wannan sunan nata shi ne: Wadda ta kai qololuwa wajen gaskiya, kuma ba ta tava yin qarya ba.
(3) DAHIRA: Dalilin da ya sa aka ambace ta da wannan suna shi ne: Akwai ruwayar da ta zo a cikin littafin Biharul Anwar juzu’i na (43) daga imam Baqir, shi ma daga iyayensa (a.s) cewa: “An ambaci Faxima ‘yar Muhammad da sunan Xahira ne saboda tsarkakarta daga dukkan datti, kuma ta tsarkaka daga dukkan qazanta, sannan ba ta yin jinin haila ko biqi”.
عن الإمام الباقر عن آبائه (ع) قال: (إنما سميت فاطمة بنت محمد: الطاهرة، لطهارتها من كل دنس، وطهارتها من كل رفث وما رأت قط يوما حمرة ولا نفسا).
Babu wani daga cikin al’ummar musulmai da yake musun saukar ayar tsarkakewa a kanta, sannan kuma tana xaya daga cikin mutane biyar da manzon Allah (s.a.w) ya lulluva musu mayafi a cikin hadisin Kisa’i.
(4) RADIYA: Ma’anar wannan suna shi ne: Wadda ta yarda da abin da Allah ya qaddara mata.

©Sheikh Mujtaba Adam kano.

SHARE:
Makala 0 Replies to “Fatima Yar Ma,aikin Allah s.a.w.a Daya Tilo”