January 4, 2024

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, ta ce tsohuwar ministar jin kai ta Nijeriya, Sadiya Umar Farouq ba ta ƙi amsa gayyatarsu ba, kamar yadda ake yaɗawa a kafafen sada zumunta.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, NAN a ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce, da gaske ne ba ta je ofishinsu ba a lokacin da suka gayyaceta, amma ta aike musu da wasiƙar cewa, ba za ta samu damar zuwa ba saboda uzurin rashin lafiya da take fama da shi.

Da gaske ne ba ta zo ofishinmu ba amma kuma ta tura mana wasiƙa kan cewa ba ta da lafiya, sannan kuma ta tura Lauyanta da ya wakilce ta a Hukumar tamu” inji shi.

©Leadership Hausa.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “”