October 10, 2023

Sin Za Ta Ci Gaba Da Taka Rawar Da Ta Dace A Harkokin Kula Da Hakkin Dan Adam a duniya

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yayin taron manema labaru na yau da kullum Larabar nan cewa, kasar Sin za ta yi amfani da damar sake zabarta a matsayin mamba a hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD, don ci gaba da taka rawar a-zo-a-gani, wajen kula da harkokin kare hakkin bil Adama a duniya, da aiwatar da ayyukan bil Adama masu yawa, da yin mu’amala da hadin gwiwa da sauran kasashe, da bayar da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban ayyukan kare hakkin bil Adama na kasa da kasa.

A jiya ne, babban taron MDD karo na 78, ya kada kuri’ar zaben wakilan kwamitin kare hakkin dan Adam na shekarar 2024 zuwa shekarar 2026, inda aka yi nasarar sake zaben kasar

 

©cri

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Sin Za Ta Ci Gaba Da Taka Rawar Da Ta Dace A Harkokin Kula Da Hakkin Dan Adam a duniya”