October 8, 2023

 

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar da cewa ta harba makamai masu linzami zuwa yankunan da Isra’ila ta mamaye, bayan harin ba-zata da mayakan Falasdinawa da ke Gaza suka kai wa sojojin gwamnatin yahudawan Isra’ila.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a safiyar yau Lahadi, Hezbollah ta ce ta kai hari kan wuraren Radar, Zabdin, da Ruwaysat Al-Alam a gonakin Shebaa da Isra’ila ta mamaye.

An kai hare-haren ne a kan yankunan na sheba’a wadanda Isra’ila ta mamaye tun bayan shigarta kasar Lebanon fiye da shekaru 40 da suka gabata, inda sanarwar ta bayyana cewa hare-haren na a matsayin kara kaimi ne domin kwatowa Lebanon sauran yankunanta da Isra’ila ta mamaye.

 

©voh

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “”