September 3, 2023

 

Ministan harkokin waje na kasar Rasha Sergey Lvrov ya ce, a aikace an fara raba hatsi ga kasashe shida na Afirka.

Kasashen da ake bai wa hatsain su ne; Burkina Faso, Afirka Ta Tsakiya, Eritrea, Mali, sai kuma Mali da Zimbabwe. Kowace kasa daga cikin wadannan kasashen za ta sami hatsin da zai kai yawan ton 50,000 a nan gaba.

Dama dai a baya Rashan ta yi alkawalin raba hatsin ga kasashen da take ganin sun fi bukatuwa da shi.

Da akwai sabani da ake da shi ka’idodin da za a yi afamin da su a tsakanin Rasha da Ukiraniya, wanda kasar Turkiya take shiga tsakani.

A halin yanzu an yin wata tattaunawar a tsakanin kasashen biyu da suke cikin halin yaki, domin sake farfadaro da wata sigar ya fitar da hatsi kasuwannin duniya, da kasar Turkiya take shiga tsakani.

 

©voh

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “”